On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Jam'iyyar APC Ta Bukaci Kotun Kararrakin Zabe Tayi Watsi Da Kalubalantar Nasarar Tinubu Daga Ja'iyyun Hamayya 3

Jamiyyar APC ta bukaci kotun sauraron kararrakin zabe dake Abuja tayi watsi da kararrakin da jamiyyun hamayya 3 suka shigar a gaban ta, inda suke kalubalantar nasarar da dan takarar jamiyyar Bola Tinubu yayi a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu.

Wannan bukata dai na kunshe ne a cikin wani martani da jamiyyar ta fitar a daren jiya Lahadi.

Da yake Magana daya daga cikin lauyoyin jamiyyar wanda Lateef Fagbemi yake jagoranta, yace jamiyyar APC ta bukaci kotun sauraron kararrakin zaben data yi watsi da kararrakin.

Jamiyyun hamayya 3 da suka hadar da AA da APM da APP a cikin mabanbantan kararraki sun kalubalanci nasarar da Tinubu yayi a matsayin zababben shugaban kasar nan.