On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Jam'iyyar APC Ta Bukaci Tsohon Gwamna Ganduje Ya Shure Gayyatar Gwamnatin Kano Kan Binciken Cin Hanci

Jam’iyyar APC a Kano ta bukaci tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje da kada ya mutunta gayyatar da Hukumar Korafe-korafen Jama’a da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano ta yi masa kan badakalar bidiyon dala.

Wata sanarwa da shugaban jam’iyyar da sakatarenta Alhaji Abdullahi Abbas da Alhaji Zakari Sarina suka sanya wa hannu, ta bayyana gayyatar da aka yi a matsayin wata manufa ta siyasa.

Sanarwar ta yi nuni da cewa gayyatar da aka yi akan wani batu da ke gaban kotu na daga cikin mugun shirin bata sunan tsohon gwamnan.