On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Jam’iyyar APC Ta ce Zata Sakawa Kwankwaso Idan Lokaci Ya yi

Jam’iyyar APC tace ‘Dan takarar shugaban kasa  na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar da dan takarar jam’iyyar Labour Peter Obi da kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP Rabi’u Musa Kwankwaso ba zasu zama barazana gad an takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Bola Tinuba ba a zaben 2023.

Mataimakin sakateren yada labarai na jam’iyyar APC Yakubu Murtala Ajaka shine ya sanar da hakan lokacin da yake zantwa dam enema labarai a Abuja.

Ajaka ya bukaci tsohon gwamnan Kano Rabi’u Musa Kwankwaso ya dawo jam’iyyar APC wadda ya bada gudunmawa wajen ginawa, yana mai cewa yafi samun yiwuwar cin zaben shugaban kasa a APC.

Haka kuma mataimakin sakataren yada labaran na APC yace duba da gudunmawa da Kwankwaso ya bayar wajen nasarar APC a zaben 2015 za’a yi masa sakayya a lokacin da ya dace idan har ya koma jam’iyyar.