On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Jam'iyyar APC Ta Gargadi Gwamnatin Kano Kan Rushe Sabbin Masarautu

SARKIN KANO

Jam’iyyar APC reshen jihar Kano, Ta gargadi gwamnatin jihar Kano kan duk wani yunkuri na rushe sabbin masarautun Kano da tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya samar, Inda ta ce matakin zai gurgunta zaman lafiyar da ake da shi a jihar Kano.

A ranar Talatar data gabata ce, Wata Kungiya mai suna ‘Yan Dan gwanlen  jihar Kano, ta  aike da wasika ga zauren majalisar dokokin jihar Kano, inda take neman a yiwa dokar data  kafa  sabbin masarautun jihar Kano gyaran fuska, Masarautun sun hada da Gaya sai Rano da Karaye da Bichi, Sannan kuma sun nemi a dawo da  tsohon sarkin kano Mohammadu Sanusi na biyu.

To sai dai a sanarwar da sakataren yada labaran jam’iyyar APC na jihar Kano Alhaji Ahmad Aruwa  ya fitar,  Ya baiyana mamakinsa kan yadda  kungiyar bata  yi korafi ba a lokacin da aka kirkiri sabbin masarautun, Inda  ya ce  kamata ya yi a rika girmama masarautu.

Jam’iyyar ta APC ta sharwaci  gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusufu  na jam’iyyar NNPP  da ya yi taka tsan-tsan  sannan kada  ya bari  a yi amfani da shi  wajen yin abunda  zai  tada zauni tsaye a jihar Kano.