On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Jam'iyyar APC Ta Raba Shugabancin Majalisar Dokoki Ta Kasa

Kwamitin gudanarwar jam’iyyar APC na kasa , Ya rarraba mukaman shugabancin zauren majalisar dokoki ta kasa na Goma da za’a kaddamar, a tsakanin shiyyoyin kasar nan.

A cewar wata sanarwa  da Sakataren yada  labaran  jam’iyyar APC na  kasa, Felix Morka  ya  fitar a ranar  Litinin,  Ya  ce yadda aka raba  mukaman  ya kunshi,  Shugaban majalisar  dattawa, Sanata  Godswill Akpabio  daga  jihar Akwa Ibom,  wanda  ya fito daga shiyyar kudu maso kudancin kasar  nan,Sai mataimakinsa,  Sanata Barau  Jibrin  daga nan jihar Kano,  wanda  ya fito  daga  shiyyar  Arewa  maso yamma  a matsayin mataimakin shugaban majalisar  dattawa.

Sauran sune, Kakakin majalisar  wakilai,Hon Abbas  Tajjudden  daga  jihar Kaduna  wanda  shima ya fito daga shiyyar  Arewa  maso yamma, Sai kuma mataimakisa Hon. Ben Kalu daga Jihar  Abiya, wanda  ya  fito  daga  shiyyar kudu maso gabashin kasar  nan.

Sanarwar  ta biyo  bayan tattaunawar da kwamitin  gudanarwar  jam’iyyar  APC na kasa  ya yi,  da kuma  ganawar da suka yi da zababben shugaban kasa Bola Tinubu da sauran masu ruwa  da tsaki, kan yadda  za’a rarraba  mukaman.