On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Jam'iyyar APC Ta Samu Nasara Akan NNPP A Gaban Kotu Kan Kujerar 'Dan Majalissar Wakilai A Kano

Kotun sauraren kararrakin zabe ta 'yan majalisar dokokin jihar dokokin jiha dana tarayya dake Kano ta soke nasarar zaben Yusuf Umar Datti, dan takarar majalisar Wakilai na Kura da Madobi da kuma Garun Malam na jam'iyyar NNPP.

Da take yanke hukuncin, mai shari’a Ngozi Azinge, ta bayyana gazawar Datti ta  yin murabus daga jami’ar Bayero dake Kano cikin kwanaki 30 kafin zaben a matsayin dalilin yanke wannan hukunci.

Ta umarci INEC da ta ajiye takardar shaidar cin zabe da aka baiwa Datti a baya tare da bayyana Musa Ilyasu Kwankwaso na APC a matsayin wanda ya cancanta ya lashe zaben.

Musa Iliyasu  Kwankwaso ya samu kuri’u mafi yawa na biyu a zaben da aka gudanar a ranar 25 ga Fabrairun  2023.