On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Jam'iyyar APC Taga Baiken Sanatocin Arewa Dake Neman Shugabancin Majalisar Dattawa

APC

Jam’iyyar APC ta kalubalanci Sanatocin da suka fito daga yankin arewacin kasar nan, dake neman kujerar shugabancin majalisar dattawa, Inda ta yi kira a gare su dasu jingine wannan aniya tasu, domin tabbatar da adalci.

Mataimakin shugaban  jam’iyyar na kasa,Salihu Lukman da kuma Kakakin jam’iyyar  Bala Ibrahim,Sunce  duk wani sanata  da  ya fito daga yankin arewacin kasar nan,kuma yake neman  kujerar  shugaban majalisar dattawa,To babu shakka bai mutunta kundin tsarin mulkin jam’iyyar ba.

Idan  za’a iya tunawa,Wasu daga cikin jiga-jigan jam’iyyar da suka fito daga yankin Kudu maso kudu da kuma Kudu maso gabashin kasar  nan,Sun bukaci a basu kujerar  shugabancin majalisar domin tabbatar da adalci ga kowane bangare na kasar nan.

Kazalika sunyi ikirarin cewar matakin shine zai nuna cewar ana yi da kowane  bangare  na kasar nan, La’akari da  yadda  jam’iyyar ta APC  ta bayar da tikitin takarar shugaban kasa  dana mataimakinsa  ga Musulmi.