On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Jam'iyyar Labour Na Duba Yiwuwar Sauya Daraktan Yakin Neman Zabenta Bayan Hukuncin Kotu

Alamu na nuna cewa  Jam’iyyar Labour na iya maye gurbin Doyin Okupe a matsayin Darakta-Janar na Majalisar Yakin Neman Shugaban Kasa a 2023 bayan yanke masa hukunci.

Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito wata majiya mai tushe a cikin jam'iyyar ta tabbatar da cewa tuni aka fara tattaunawa domin maye gurbin Okupe.

Majiyar ta kara da cewa duk wadanda abin ya shafa za su dauki matakin tare da shi kansa Okupe.

A ranar Litinin ne aka samu Okupe da laifin karbar kudi naira miliyan 240 daga hannun tsohon mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Sambo Dasuki, kuma daga karshe aka yanke masa hukunci.