On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Jam'iyyar Labour Ta Kori Doyin Okupe Daga Cikinta

DOYIN OKUPE

Jam’iyyar LP reshen jihar Ogun, Ta kori Babban daraktan kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar, Dr Doyin Okupe daga cikinta.

An kori  Okupe tare da wadansu mutane 10 daga cikin jam’iyyar, bayan an zarge shi  da kin sabunta  shaidarsa  ta zama dan jam’iyyar  a watanni shida da suka gabata, wanda hakan ya sabawa kundin tsarin mulkin jam’iyyar.

An cimma wannan matsaya ne a yayin taron da jam’iyyar ta gudanar a sakatariyarta  dake birnin Abeokuta a ranar Alhamis, inda suka yi  kira  da a gaggauta samar da daraktan yakin neman zaben jam’iyyar  na yankin Arewa, domin tabbatar da samar da daidaito da kuma ingantaccen tsari na siyasa.

Shugaban jam’iyyar Labour, reshen jihar, Michael Ashade, Ya  ce an dauki matakin ne domin ladabtarwa, sannan kuma ya zargi Mister Doyin Okupe da raba kan jam’iyyar  a  jihar.