On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Jam'iyyar LP Ta Peter Obi Ba zata Iya Cin Zaben Shugaban Kasa Ba, Inji Kwankwaso.

Peter Obi Da Kwankwaso

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Kwankwaso, ya bayyana dalilin da ya sa ba zai iya zama abokin takarar tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi ba a zaben shugaban kasa da ke tafe.

Ya ce mutane ba sa ji dadin yawancin abubuwan da ke faruwa a Kudu maso Gabas, saboda  haka zai yi wahala ’yan Arewa su kada kuri’a yadda ya kamata ga  wani dan takara da ya fito daga yankin daga kowace jam’iyya.

Sai dai dan takarar shugaban kasar na jam'iyyar NNPP, bai kawar da yiwuwar kulla kawance da takwaran nasa na jam'iyyar Labour ba, amma dai idan Obi ya amince ya zama mataimakinsa.

Sai dai ya kawar da yiwuwar ko  jam'iyyar Labour zata iya lashe zaben shugaban kasa saboda goyon bayan da aka fi samu a wani yanki ne kawai kuma yawan alkaluman  da ke can ba za su iya kawo kujerar shugaban kasa ba.