On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Jam'iyyar NNPP Na Neman Kawo Karshen Yarjejeniyar Da Kwankwasiyya

Jam’iyyar NNPP ta rubutawa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC wasika akan shirin da wasu mutane ke yi na sauya tambarin jam’iyyar.

Jam’iyyar ta kuma rubutawa Sanata Rabi’u Kwankwaso, dan takararta na shugaban kasa wasika, domin ya kawo karshen yarjejeniyar fahimtar juna da ta shiga da kungiyar Kwankwasiyya.

Duk wasikun biyu dai sun samu sahannun lauyan jam’iyyar, Mista Peter Ogah, a  jiya laraba.

Idan za a iya tunawa dai a ranar 5 ga watan Satumba ne wani bangare na jam’iyyar ya kori Kwankwaso bisa zarginsa da zagon kasa, amma a  ranar aka samu umarnin kotu wanda ya hana dakatarwar da aka yi masa.

…….