On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Jam'iyyar NNPP Ta Zargi Gwamnatin Kano Da Sawa A Kama 'Ya'yanta

NNPP

Jam’iyyar NNPP reshen jihar Kano, Ta yi barazanar janye goyon bayan ta akan yarjejeniyar samar da zaman lafiya data saka hannu akan ta, saboda zargin da ta yi na cewar jami’an ‘yansanda da kuma gwamnatin jihar kano na kulla wata makarkashiya na tsoratar da ‘yan takarar dake cikin jam’iyyar.

Jam’iyyar  ta yi  zargin  cewar  rundunar  ‘yansandan jihar  Kano  ta karbi wani umarni  daga hannun gwamnatin jihar  Kano, inda  suka yi wani shiri  ta karkashin kasa  domin a rika  kama  jiga-jigan  jam’iyyar  ta NNPP a kananan hukumomin jihar Kano 44.

Dan takarar  sanatan kano ta  Arewa a karkashin jam’iyyar  ta NNPP,  Dr Baffa Bichi ne ya baiyana haka a yayin wani taron manema Labarai da aka shirya a sakatariyar    jam’iyyar dake nan Kano.

Ya kuma yi ikirarin cewar  suna  da hujjoji  na sunayen  ‘yan jam’iyyar  NNPP  da za’a kama.

Har kawo wannan lokaci  dai rundunar  ‘yansandan jihar kano  bata  mayar da martani  akan  zargin ba.