On Air Now

Off Air

Noon - 6:00pm

Jam'iyyar PDP A Jihar Legas Ta Shirya Kai Korafi Gaban Hukumar DSS Kan Zargin Cin Zarafi Musgunawa Daga Jam'iyyar Mai MulkiJam

Jam’iyyar PDP reshen jihar Legas da kwamitin yakin neman zaben Jandor  sun kammala shirye-shiryen kai kara zuwa hukumar DSS da sauran hukumomin tsaro kan hare-haren da ake kaiwa magoya bayanta a sassan jihar  Legas.

 

Jam’iyyar ta kuma sha alwashin cewa ba za ta lamuni duk wata musgunawa da cin zarafi ga magoya bayanta ba, tana mai cewa wadanda aka samu da laifi ba za’a kayale su haka ba.

Daraktan tsare-tsare na Majalisar Yakin Neman Zaben Jandor, Hon Niyi Adam shine ya bayyana hakan bayan magoya bayan jam’iyyar suka yi wa tawagar majalisar da sakatariyar jam’iyyar bayani a kan zargin lalata musu kayyaki da magoya bayan jam’iyya mai mulki suka yi.

Sai dai jam’iyyar APC mai mulki ta bakin sakataren yada labaranta, Seye Oladejo, ya wanke jam’iyyarsu daga hare-haren da ake kai wa ‘yan adawa, yana mai cewa jam’iyyar ba ta da dalilin kai wa ‘yan adawa hari domin tana da tabbacin samun nasara a dukkan zabuka.