On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Jam'iyyar PDP Ta Bukaci Hukumar Zabe Ta Shirya Sabon Zabe Kan Kujerun 'Yan Majalisa 27 Da Suka Koma APC A Ribas

PDP

Jam’iyyar PDP ta lashi takobin rubutawa hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta kokenta a yau Talata, domin neman a sake gudanar da sabon zabe, wanda zai bada damar canza ‘yan majalisar dokokin jihar Ribas guda 27, da suka sauya sheka zuwa jam’iyyar APC a jiya.

A ranar  Litinin ne  yan  majalisa 27 na jam’iyyar PDP  suka  sanar da komawarsu jam’iyyar APC, tare  da yin barazanar  yin fatali da bukatun da gwamnan jihar Ribas Sim Fubara  ya gabatar masu.

Ana zargin sauyin shekar da  ‘yan majalisar dokokin jihar suka yi, nada alaka  da yakin cacar baka dake  wakana tsakanin  gwamnan da ministan Abuja  Nyesom Wike.

Da yake tsokaci  kan canza  jam’iyyar  da suka yi,  Sakataren yada labaran jam’iyyar  PDP  na kasa, Debo Olugunagba, ya fadawa manema labarai a daren jiya  cewar, Jam’iyyar  zata yi amfani da matakan da suka dace domin kwato kujerun nata.

Ya kuma aiyana  kujerun ‘yan majalsiar  guda  27 da suka canza  jam’iyya a matsayin wadanda babu kowa a  kansu, kamar  yadda yake  bisa sashi na  109  daya  cikin baka da  Ga  cikin baka, na kundin tsarin mulkin kasa da aka yiwa  gyaran fuska.