On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Jam'iyyar PDP Ta Caccaki Jam'iyyar APC Kan Yawan Bashin Da Ake Bin Najeriya Wanda Ya Haura Tiriliyan 41

PDP DA APC

Jam’iyyar PDP ta caccaki shugaban jam’iyyar Apc na kasa, Abdullahi Adamu, kan Kalaman da yayi na cewa gwamnatin tarayya zata iya cigaba da ciwo bashi daga yanzu har Illa Masha Allah.

A yayin wata hira da aka yi dashi ta cikin wani  shiri a gidan talabijin na Trust a ranar Litinin, Adamu ya ce kasashe irin su Amurka da Ingila suna karbar lamuni daga cibiyoyin hada-hadar kudi na duniya domin biyan bukatunsu.

Ya kara da cewa kamar sauran kasashe, Najeriya na iya cin bashi a kowane  lokaci  domin  bunkasa samar  da   ababen more rayuwa.

Da yake mayar da martani kan kalaman da shugaban jam’iyyar  APCn yayi,  kakakin jam’iyyar PDP, Debo Ologunagba, ya ce bai dace shugaban jam’iyyar ya kafa  hujja da cewar ana ciwo bashin ne domin yin abubuwan da zasu amfani kasa.

 A yanzu haka dai  bashin kasashen waje da ake bin Najeriya  ya haura tiriliyan   41 da bilyan  60.