On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Jam'iyyar PDP Ta Maka APC Kotu

TAMBARIN APC DA PDP

Jam’iyyar PDP ta kai kara gaban wata kotu, inda take bukatar a tursasawa Hukumar Zabe ta kasa mai zaman kanta ta hana Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu da kuma na jam’iyyar LP Peter Obi, sauya sunayen wadanda zasu yi masu takarar mataimaki.

Kazalika jam’iyyar ta PDP ta bukaci Kotu ta soke takarar  Tinubu da Peter Obi, har sai idan  sunyi takarar ne tare  da mutanen da suka fara baiyanawa a matsayin mataimakansu, wanda suka hada Kabiru Masari da Kuma Doyin Okupe.

A cikin kunshin karar, Jam’iyyar PDP na bukatar kotu ta bayar da wani umarni wanda zai hana hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta  saunya sunayen yan takarar mataimaki na Tinubu da kuma peter Obi.

Jam’iyyar ta ta dogara ne da cewa babu wani mai kama da tsarin Dan takara na wucin gadi, Da Yan Najeriya suka sa dashi.