On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Jam'iyyar PDP Ta Nada Damagum Amatsayin Shugaban Riko Na Kasa

Kwamitin gudanarwa na jam’iyyar PDP na kasa ya nada Umar Damagum, amatsayin shugaban rikon kwarya da zai kula da harkokin jam’iyyar.

Sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP na kasa, Debo Ologunagba, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a ranar Talata, a sakatariyar jam’iyyar dake Abuja.

Damagun zai maye gurbin Iyorchia Ayu a matsayin shugaban jam'iyyar na kasa, bayan dakatar  da Ayu.