On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Jam'iyyar PDP Ta Shiga Tsaka Mai Wuya A Jihar Ogun

TAMBARIN JAM'IYYAR PDP

Wata Babbar Kotun taraiyya mai zamanta a birnin Abeokutan jihar Ogun, ta soke daukacin zaben fidda gwani na ‘yan takara daban-daban da jam’iyyar PDP ta gudanar, Gabanin Babban zaben shekara mai zuwa.

Mai shari’a  O.O Oguntoyinbo  ne  ya  bada umarnin, lokacin da yake zartar da hukunci akan shari’ar, wadda wasu  ‘ya’yan jam’iyyar  Taiwo Olabode idris da Kehinde Akala da kuma Alhaji  Ayinde Monsuri  suka shigar gaban kotun, sun kalubalantar sunayen wakilan jam’iyyar da aka yi amfani dasu a yayin zaben  fidda  gwani da jam’iyyar  ta gabatar.

Zaben  fidda gwanin da kotun ta soke sun hada, Dana  Gwamna sai yan majalisar dattawa da ‘yan majalisar wakilai da kuma na yan majalisar  dokokin jihar ta Ogun, A bisa haka ne kotun ta bada umarnin sake  gudanar da sabon zaben fidda  yan takara  nan da  kwanaki  14 masu zuwa.

Bugu da kari kotun  ta  haramtawa  hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta cigaba da aiyana Hon Ladi Adebutu  a matsayin dan takarar gwamnan jihar  ta Ogun karkashin jam’iyyar  PDP.