On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Jam'iyyar PDP Ta Zargi APC Da Boye Sabbin Kudi Domin Sayen Kuri'a

PDP

Jam’iyyar PDP ta zargi jam’iyyar APC mai mulkin kasa da boye sabbin takardun kudi da aka sauyawa fasali, domin siyan kuri’a a zabe mai zuwa.

A wata sanarwa  da  kakakin jam’iyyar  na kasa,Debo  Ologunagba  ya fitar  a ranar Lahadi,Ya ce  kunchin da  jam’iyyar  APC  ta jefa  kasar nan, zai zama tarihi, idan aka zabi  Atiku  Abubakar a matsayin shugaban kasa.

Jam’iyyar  ta  PDP  ta yi kira  ga babban  bankin kasa,  da yayi hankali da  yadda  jama’ar  kasar  nan   suka samu kansu a  ciki.

Bugu da kari  ta  yi kira  ga  Bankunan kasar  nan dasu dauki matakan  da suka dace  na kawo karshen matsalar rashin kudi da jama’a suke a ciki,  da kuma sanya ido kan yadda ake rarraba  kudin a tsakanin jama’ar kasa.