On Air Now

ZANGON RANAR ASABAR

Noon - 6:00pm

Jam'iyyar PRP Na Barazanar Daukar Matakin Shari'a Akan Bankin CBN

Jam’iyyar PRP ta gaza tasarrafi da kudadenta sakamakon sabon tsarin harkokin kudi a Najeriya, ta kuma yi barazanar daukar matakin shari'a kan CBN a gaban Kotu.

PRP dai ta zama ta farko  da ta fara ji a jikinta ta hanyar tasirin sabon  tsarin  kuɗi na babban bankin kasa CBN  a tsakanin jam’iyyun siyasa, ta kuma yi tsokaci kan yadda tsarin ya jawo wa ‘yan Najeriya wahalhalu, inda ta ce ta gaza  samun kudaden da ta adana domin zabe mai zuwa. 

Saboda  haka jam’iyyar ta yi barazanar neman diyya a gaban  kotu daga CBN.

Shugaban jam’iyyar PRP na kasa, Alhaji Falalu Bello, ya bayyana haka a lokacin gabatar da kundin manufofin  jam'iyyar ga manema labarai a Abuja. 

Jaddawalin manufofin  dauke da kudurori shida, ya tabo batun sake fasalin tattalin arziki da inganta ilimi da bunkasa  hadin kan kasa da tsarin tarayya na gaskiya da  inganta tsaron kasa da farfado da masana'antun hakar mai da man fetur da  iskar gas da ma'adanai.

Bello ya ce janye sama da Naira Tiriliyan 2 da suke jagawwa a hannun jama'a da kuma buga Naira biliyan 300, shine makasudin  hamudani da  ake fuskanta a Najeriya.