Jam'iyyun adawa a Najeriya sun soki gwamnatin tarayya kan amincewar da Fadar Shugaban Kasa ta yi cewa akwai yiwuwar 'yan ta'adda sun dasa jami'an su a cikin hukumomin tsaro.
A wata sanarwa ta hadaka, jam'iyyun sun ce hakan na nuna yadda matsalar tsaro ke kara tabarbarewa a kasar.
Jam'iyyun sun bukaci gwamnati da ta gaggauta gano wa tare da cafke duk wani jami'i ko mutum da ake zargi da taimakawa kungiyoyin 'yan ta'adda, suna masu cewa rashin daukar kwakkwaran mataki zai kara raunana yunkurin da ake yi na magance matsalar tsaro.
Da yake magana, Sakataren Yada Labarai na Jam'iyyar African Democratic Congress (ADC), Bolaji Abdullahi, ya ce ikirarin cewa 'yan ta'adda sun kutsa cikin hukumomin tsaro ya kamata ya zama abin da zai jawo bincike mai zurfi, domin gano masu hannu a lamarin da kuma hukunta su bisa doka.
Shi ma Sakataren Yada Labarai na Jam'iyyar Social Democratic Party (SDP), Rufus Aiyenigba, ya ce idan har gwamnati ta tabbatar da zargin, ya zama wajibi ta dauki matakin gaggawa wajen kamo wa da gurfanar da duk wanda ke taimaka wa 'yan ta'adda, yana mai gargadin cewa duk wani jinkiri zai kara dagula matsalar tsaro.
Wannan martani ya biyo bayan kalaman Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai da Dabaru, Daniel Bwala, wanda ya bayyana cewa akwai yiwuwar cewa akwai 'yan ta'adda a cikin wasu sassan hukumomin tsaro, tare da tabbatar da cewa gwamnati na daukar matakan da suka dace domin shawo kan lamarin.
Comments
Add a comment