On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Jam'iyyun PDP Da Labour Na Gargadi Kan Jinkirin Kamawa Da Hukunta Kwamishinan INEC Na Jihar Adamawa

Jam’iyyun PDP da Labour sun gargadi ‘yan sanda da INEC kan jinkirta kamawa tare da gurfanar da kwamishinan zabe  na jihar Adamawa Hudu Yunusa-Ari, biyo bayan ayyana ‘yar takarar gwamna a jam’iyyar APC, Aishatu Dahiru a matsayin wadda ta lashe zaben gwamna a jihar ba bisa ka’ida ba.

Jam’iyyun adawar dai sun ce ba zasu lamunci yin Ha’inci  ba, sun kuma yi kira da a gudanar da bincike na gaskiya kan al’amarin.

Hakazalika, gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya dage kan cewa dole a gudanar da bincike akan kwamishinan zaben.

Mataimakin sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP na kasa, Ibrahim Abdullahi ya zargi jam’iyyar APC da laifin tabarbarewar al’amura a jihar  Adamawa, yana mai bayyana abin da kwamishinan  ya yi a matsayin cin amanar kasa.

Har ila yau, babban mai magana da yawun majalisar yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Yunusa Tanko, ya bayyana damuwarsa kan yadda Yunusa Ari ke cigaba da yawo a matsayin ‘yantacce kwanaki kadan bayan abin kunya da ya aikata.