On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

JIGON RAHOTONMU A WANNAN MAKON

IDON MIKIYA

A irin wannan lokaci, cikin shekarar da ta gabata, babu wani kwakwaran hijabi tsakani mamakon ruwan sama da asibitin garin Gabasawa dake nan Kano, bayan da wani dan kwangila da ba a sake jin duriyar sa ba ya yaye kwanon rufin sa da nufin yin gyara.

A duk lokacin da ni’imar All ta sauka, fallen jikakken sili da ya rage a saman ginin baya hana ruwan sama cika asibitin makil.

Wannan al’amari kan sabbabawa ma’aikatan asibitin kwashe wasu awanni suna aikin kwarfe tulin ruwan da ya taru kafin gudanara da aikin duba marasa lafiya sama da 200 dake ziyartar sa a kowacce rana.

Samun labarin wannan al’amari daga guda daga cikin masu saurare ke da wuya, Arewa Radio ta niki gari domin ganewa idon ta. kuma mako guda bayan bayan fitar da rahoton, aka kama aiki gada-gadan domin gyara al’amarin.

Duk da cewa an samu takaddama kan bangaren da ke da alhakin gudanar da aikin tsakanin dan majalisar tarayya mai wakiltar yankin da kuma gwamnatin jihar Kano bayan fitar da rahoton, wasu masu ruwa da tsaki a garin sun yi kokari wajen samar da maslaha tare da mikawa dan majalisar, Nasiru Auduwa damar yin aikin.

Yayinda muka sake komawa domin ganin halin da asibitin ke ciki, la’akari da yanayin damunar da muke ciki yanzu haka, ma’aikata da kuma al’umar garin sun bayyana farin cikin su. Shima wakilin mai garin yankin ya bayyana jin dadin sa bisa cigaban da aka samu.

Shugabar asibitin, ta mana bayanin cewa sakamakon gyaran da aka yi, yanzu haka sun samu damar canza inifom din su ba tare da fargabar cewa zasu sake dafewa kamar wadancan sakamakon daudadden ruwan sama dake zuba a2kan su.

To sai dai yayinda masu ruwa da tsaki ke jaddada farin cikin su, har yanzu akwai sauran rina a kaba dangane da nagartar asibitin, wanda sama da mutane 2000 ke dogara akan sa wajen samun kulawar lafiya a kowanne wata.

Misali, ya zuwa yanzu, asibitin dake duba dumbin marasa lafiya, ciki harda karbar haihuwa ba shi da likita ko da guda. Binciken mu ya tabbatar da cewa mafi girman kwarewa cikin ma’aikatan da asibitin ke da shi a adaidai wannan lokaci ita ce jami’ar kula da lafiyar al’uma.

Da yake magana akan batun, sakataren karamar hukumar gabasawa, wanda yayi magana a madadin shugaban karamar hukumar, Mahe Garba Garundanga, yace tuni aka fara shirye-shiryen samar da kwararren likita a asibitin.

Akan batun samar da ruwa da wutar lantarki kuwa, shugaban kungiyar matasa da samar da cigaban yankin, Idris Wa’izi Gabasawa ya tabbatar da cewa dan majalisar tarayya na yankin, Nasiru Auduwa ya bukaci kungiyar da ta gabatar masa da kiyasin abinda sauran aikin zai ci, domin daukar matakin gaggawa, yana mai kara da cewa ba shi da labarin cewa ba a kammala aikin ba.