On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Jigon Rahotonmu Na Wannan Makon, Halin Da Yajin Aikin ASUU Ya Jefa Dalibai A Kano

TAMBARIN IDON MIKIYA NA AREWA RADIYO

A yayin da har yanzu, mafi akasarin Daliban Jami’oi basu kaiga murmurewa daga lahanin da yajin aikin kungiyar Malaman Jami’oi ta kasa ASUU, da aka janye kwanan nan yayi masu ba, Sai dai kuma a iya cewa, ta wani bangaren yajin aikin ya zama wani abun tagomashi ga wadansu daliban a nan Kano.

Daliban, Sun baiyana wasu daga  cikin kalubalen da suka  fuskanta  daga bangaren abokansu da kuma sauran jam’ar gari, dama yadda suka yi amfani da lokacin yajin aikin ,  wajen kirkirar  wata manhaja  da  zasu  magance  kalubalen.

Irin wadannan kirkire-kirkire  da  Daliban suka  bijiro  dasu  a lokacin da ake  yajin aikin na ASUU, sune abubuwan da rahotonmu na musamman a wannan makon, da wakilinmu, Kamaludden Muhammad  ya  hada mana  yayi duba a kai.

Ga shi kuma da cigaban rahoton  da  ya hada mana.

Latsa kasa domin jin cikakken rahoton

More from Labarai