On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Jihohi 17 Sun Kashe Sama Da Naira Milyan Dubu 65 Akan Yaran Da Basa Zuwa Makaranta

Yara

wani bincike ya nuna cewa, Jihohi 17 na kasar nan sun karbi tsabar kudi har naira Milyan Dubu 65 da Milyan 46 domin dakile matsalar yawan yaran da basa zuwa makaranta daga shekarar 2019 zuwa 2021, a matsayin wasu kudaden tallafi da ake samu ta karkashin wani shirin bankin duniya.

Wani kundin bayanai da aka samu daga Hukumar Ilimin Bai Daya ta kasa, Ya baiyana cewa jihohin da suka amfana da shirin, sun kunshi jihohin Arewa Maso yamma 13 dana Shiyyar Arewa maso gabas da kuma jihohin Niger da Oyo da Ebonyi da kuma jihar Ribas.

A kididdigar da Ma’aikatar Ilimi ta kasa ta fitar a watan Nuwambar Bara, ta baiyana cewa a karkashin shirin an komar da yaran da basa zuwa makaranta kimanin Dubu 924 da 590.

Sai dai kuma duk da haka har yanzu akwai damuwa kan yadda ake samun karuwar yaran da basa zuwa makaranta A Najeriya.