Wani mai sharhi kan al’amuran yau da kullum a Kano, Comrade Ishaq Ja’afar Gandun Albasa, ya yi kira ga Majalisar Dokokin Jihar Kano da ta gaggauta tattaunawa tare da amincewa da kudirin dokar yaki da shan miyagun kwayoyi da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya aike mata.
A cikin wani sakon murya da ya aikewa Arewa Radio, Ja’afar ya ce rundunar hadin gwiwar hukumomin yaki da shan miyagun kwayoyi da fataucinsu ta jihar Kano na bukatar cikakken goyon bayan doka domin gudanar da ayyukanta yadda ya kamata.
Ya kuma bukaci rundunar da ta kafa sashen ba da shawarwari da jagoranci, domin gano musabbabin da ke sanya matasa fadawa kangin shaye-shaye da kuma samar musu da hanyoyin gyara da ya dace da kowannen su kafin sake dawo da su cikin al’umma.
Ja’afar ya kuma bukaci a sassauta hukunci ga wadanda suka fara aikata laifin shaye-shaye, yana mai cewa daure su a gidan yari da sauran hukunci mai tsanani na iya lalata makomarsu da basirarsu.
Ya kuma bukaci gwamnati da ta kafa ofisoshin kwamitin a sanatoriyoyi guda uku dake Kano tare da nada kwararrun tsoffin jami'an tsaro su jagorance su domin karfafa aiyukan kwamitin da kuma kara matsar da sha da fataucin miyagun kwayoyin kusa da al'uma.
Bayanin nasa na zuwa ne a lokacin da shugaban kwamitin, Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado, ya zargi Majalisar Dokokin Kano da rashin daukar batun yaki da shan miyagun kwayoyi da fataucinsu da muhimmanci, sakamakon jinkirin da ya ce majalisar ke yi wajen fara tattaunawa kan kudirin dokar.
Sai dai a martanin da ta fitar, mai dauke da sa hannun kakakin ta, Kamaludden Sani Shawai, majalisar ta musanta zargin, tana mai cewa ta fara bin matakan da suka dace, sai ta jinkirta saboda tattaunawa akan kasafin kudin shekarar 2027 ya danne wannan bukata, musamman la'akari da cewa aiyukan gwamnati ba sa gudana ba tare da kasafin kudi ba.
Comments
Add a comment