On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Jirage Zasu Rika Biyan Diyya Ga Fasinjojin Da Suka Yi Jinkirin Tashin Su.

FESTUS KEYAMO

Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo, Ya ce hukumomi dake kula da harkokin sufurin jiragen sama a kasar nan zasu fara tilastawa kanfanonin jiragen sama biyan diyya ga fasinjojin da suka fuskanci tsaikon tashin jirginsu, ko kuma aka soke tashin jirgin baki dayansa, daga watan janairun sabuwar shekara ta 2024.

Ministan ya baiyana haka ne a lokacin da ya baiyana gaban hadakar kwamitin kula  da sufurin jiragen sama na zaurikan majalisun dokokin kasa, domin kare kudirin kasafin kudin ma’aikatarsa.

Ya  ce za’a yi  ragin kudin tikiti ga fasinjojin da suka fuskanci tsaikon tashin jirginsu a wani  bangare na biyansu diyya.

Ministan ya kuma bada tabbacin cewar  za’a rika wallafa sunayen jiragen  da suka yi jirgin tashin fasinjojinsu a kafafen yada labarai a kowane  mako.