On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Jirgin Emirates Zai Rage Zirga-Zirgarsa A Najeriya Saboda Harajin Dala Milyan 85 Da Gwamnati Ke Binsa

HOTON JIRGIN EMIRATES

Kanfanin jiragen sama na Emirates zai rage zirga-zirgarsa a kasar nan sakamakon gazawarsa wajen bawa gwamnatin Najeriya Harajin Dala Milyan 85.

Kanfanin ya baiyana haka ne, ta cikin wata wasika da ya aikewa ministan sufurin jiragen sama na kasa, Hadi  Sirika,  a ranar  22 ga watan da muke bankwana  dashi.

Mataimakin shugaban shiyya na kanfanin jiragen saman Emirates, Sheik Majid Al Mualla, Yace  rage zirga-zirgar kanfanin a kasar nan zata  fara aiki ne daga ranar 15 ga watan Gobe.

Sanarwar  ta kara da cewa za’a rage  sauka da tashin jiragen saman Emirate  daga kaso 11 bisa  100 zuwa Kaso 7 bisa 100  a filin tashi da saukar jiragen sama na Murtala Muhammed dake Ikko.