On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Jirgin Farko Na Maniyatan Kano 400 Sun Ya Isa Kasar Saudiyya

Cikin daren da ya gabata ne kashin farko na maniyyata 400 daga jihar Kano suka tashi daga filin jirgin sama na Malam Aminu Kano zuwa kasar Saudiyya.

Da yake bankwana da maniyatan, Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje, ya bukace su da su kasance jakadu nagari na jihar Kano da Najeriya baki daya.

Ganduje wanda ya samu wakilcin Mataimakin sa, Dr Nasiru Gawuna ya kuma yi kira garesu su gudanar da addu’o’in neman zaman lafiya da tsaron kasa.

Babban Sakataren Zartaswa na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Ambasada Mohammed Abba Danbatta, ya  shawarci maniyata da su rika kashe kudadensu ta hanyar  bin ka’idojin da aka koya musu a lokacin bita.

Kashin farko na maniyatan Kano sun kunshi maza 292 da mata 108.