On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Jirgin Max Air Zai Fara Dawo Da Alhazan Najeriya Gida A Ranar Asabar

MAX AIR

Daya daga cikin kanfanonin jiragen saman da suka yi jigilar Alhazan Najeriya a Aikin Hajjin Bana, Max Air , Yace zai fara jigilar dawo da alhazan kasar nan daga kasa mai tsarki a ranar Asabar

Wata sanarwa da kakakinsa, Ibrahim Dahiru ya fitar jiya a Abuja, Yace  Alhazan  jihar Borno sune za’a fara kwasowa  zuwa gida Najeriya.

Hukumar aikin hajji  ta kasa,  ta  dora  alhakin jigilar  Alhazai  dubu  16  da suka fito  daga jihohi  13 akan kanfanin jiragen sama na Max Air a aikin hajjin bana.

Jihohin sun hada da Borno sai Adamawa da Bauchi da Gombe da Taraba da Niger da Kogi Da jihar Kwara Da Jigawa da Katsina da Benue sai Jihar Filato da Kuma jihar Nasarawa.