On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Jirgin Rundunar Sojin Sama Ta Kasa Ya kai Wani Hari Bisa Kuskure A Jihar Katsina

Jirgin Sojin Saman Najeriya

Wani abun alhini ya sake faruwa ranar Laraba a jihar Katsina, A yayin da wani jirgin Yaki dake fakon ‘Yan Ta’adda yayi kuskuren kai hari akan al’ummar gairn Kunkuna dake cikin karamar hukumar Safana ta jihar Katsina.

Duk da cewar  har kawo yanzu babu cikakkun bayanan yadda abun alhinin ya faru a kauyen na kunkuna, Sai dai jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa mutane da dama ne suka mutu a sakamakon harin da jirgin yakin yakai.

Rahotanni sun baiyana cewa jirgin yakin yayi kuskuren kai harin ne bayan da  ya zaci wajen  nan inda  sansanin ‘yan Ta’addar yake.

Wannan al’amari na zuwa ne a yayin da ‘yan bindiga suka halaka wani jami’in Dan Sanda  mai matsayin Mataimakin Kwamishinan Yansandan Aminu Umar a ranar  Talata a dai karamar hukumar ta Safana dake jihar Katsina, Kazalika a ranar ne kuma aka kaiwa ayarin jami’an  shugaban kasa hari a dai jihar ta Katsina.

Har kawo wannan lokaci rundunar sojin sama ta kasar nan bata mayar da martani akan  harin ba.