On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Ka aiwatar da alwashin gyara Najeriya - Kungiyar Afenifere ta yi ga Buhari

Sai dai kungiyar Yarabawan ta bada shawarar cewa domin tabbatar da hankoron


Kungiyar Yarabawa ta Afenifere ta kalubalanci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aiwatar da alwashin da ya yi na kakkabe matsalolin Najeriya a zahiri kuma a aikace.

Da yake karbar sabbin shugabannin cibiyar kwararrun Akantoci ta kasa ICAN a Abuja, shugaban kasa Buhari ya jaddada aniyar gyara Najeriya daga halin da take ciki..

Sakataren yada labaran kungiyar ta Afenifere Mr Jare Ajayi ya yabawa shugaban kasa Buhari bisa amincewa da ya yi cewa akwai matsaloli da ake bukatar kawar da su a Najeriya.

Sai dai kungiyar Yarabawan ta bada shawarar cewa domin tabbatar da hankoron shugaban kasar na gyara Najeriya musamman a bangaren tsaro, akwai bukatar a kyale duk wata jiha da take muradi ta samarwa kanta ‘yan sandan jahohi.