On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Kalli Yadda Aka Kai Sheikh Abduljabbar Kotu A Yau

Yanzu haka an jibe jami'an tsaro a inda za'a yanke hukuncin.

Mai Sharia Ibrahim sarki yola na Babbar kotun shari'ar musulunci dake kofar Kudu ne zai jagoranci yanke hukuncin.

Wakilinmu Bashir Faruk Durumin iya ya ce an jibge jami'an tsaro a kan titin zuwa fadar sarkin Kano Kuma an Hana bi ta gurin.

Ana zarginsa da yin kalaman batanci ga fiyayyen halitta annabi Muhammad Sallallahu alaihi wasalam.