On Air Now

Maraicen Asabar

6:00pm - Midnight

Kanfanin Jiragen Sama Na Kasa Na Dab Da Fara Aiki

HADI SIRIKA

Ministan sufurin jiragen sama na kasa,Sanata Hadi Sirika Ya ce nan bada jimawa ba ,kanfanin jiragen sama na kasa zai fara gudanar da aiki.

Ministan ya baiyana cewa  gwamnatin taraiyya   ta  kammala  matakin  farko  na ganin kanfanin jirgin saman ya fara aiki, a  yayin da yanzu ya rage  samun  lasisin  zirga –zirgar  da  jiragen  zai rika  yi.

Da  yake  yiwa manema Labarai  na fadar  shugaban kasa  jawabi, jim kadan bayan kammala  zaman  majalisar  zartawa  na kasa  a  jiya, Ya  ce  tuni suka samu jiragen kuma har an yi masu  fenti  da  tambarin kasar nan.