On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Kanfanin KEDCO Ya Nemi Afuwar Abokan Huldarsa Kan Karancin Wutar Lantarki

KEDCO

Kanfanin rarraba hasken wutar lantarki na KEDCO Ya bukaci abokan huldarsa dake jihohin Kano da Katsina da Kuma Jigawa dasu kara yin hakuri, a yayin da kanfanin ke bakin kokarinsa domin inganta samar da hasken wutar lantarki a jihohin ukku.

Shugaban sashin kasuwanci na kanfanin, Abubakar Yusuf ne yayi wannan roko lokacin da yake zantawa da manema Labarai a shalkwatar kanfanin dake nan Kano.

Y ace  kanfanin yana sane da irin rashin jin dadin da abokan huldarsa suke  ciki a saboda  karancin wutar  lantarkin da ake samu musamman a wannan lokaci na azumin watan Ramadan.

Ya kuma baiyana cewar  a yanzu haka kanfanin na daukar wasu  matakai domin magance  matsalar  cikinsu hadda  gyara  Taransifomomin da suka samu matsala domin inganta  samarwa da kuma rarraba  wutar lantarkin.