On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Kanfanin Mai Na Kasa Ya Ce Farashin Mai Ba Zai Karye Ba

Kanfanin sarrafa Albarkatun mai na kasa NNPCL, Ya baiyana cewar matatar mai ta Dangote da ta Fatakwal da kuma sauran wadanda ake dasu, ba zasu sa a samu sauyin farashin man fetir ba.

Shugaban kanfanin, Mele  Kyari  ne ya baiyana haka, yayin  wata hira da aka yi da shi a gidan Talabijin na kasa,  inda  ya  yi  watsi  da kalaman  da ke  cewar  za’a  samu saukar  farashin man,  kasancewar  suma  matatun  zasu  rika  lissafin kudin da zasu kashe  wajen aikin tace  man, da sauran wasu  batutuwa.

Ya kara da cewar  matatar  mai  ta  Fatakwal  zata cigaba da aiki  daga watan Disamba  mai zuwa, sannan  kuma  duk  tunanin  da ake na samun  saukin farashin man  saboda  man da  Matatar  mai  ta Dangote  zata  rika  tacewa,  hakan ba zaisa   farashin nasa  ya sauka ba.

Kazalika  ya  tabbatar da  cewar  bayanan  farashin mai  na kowace  jiha  da aka  ga yana yawo a shafukan sada  zumunta,  sun fito ne  daga  kanfanin man  na  kasa.