On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Kanfanonin Indiya Zasu Zuba Jarin Dala Bilyan 14 A Najeriya

Tinubu a Indiya

Ziyarar da shugaban kasa Bola Tinubu ya kai kasar Indiya ta fara haifar da ‘Da mai ido, A yayin da tun kafin dawowar shugaban kasar gida, wasu Kanfanonin Indiya guda hudu suka yi alkawarin zuba jarin Dala Bilyan 14 a kasar nan. Kanfanonin sun hada Indorama Petrochemical Limited da Kanfanin sarrafa karafa da samar da lantarki na Jindal Steeel anda Power Limited.

An kulla yarjejeniyar zuba jarin ne a yayin wata ganawa da aka yi  tsakanin  masu kanfanonin da shugaban kasa  a ranar Laraba, kamar yadda yake kunshe a wata sanarwa da kakakinsa  Ajuri Ngelale  ya fitar.

Bola Tinubu ya yabawa  kanfanonin  tare da bawa  ‘yan kasashen waje masu sha’awar  zuba jari a kasar  nan  tabbacin samun  riba  mai ma’ana a kasuwancinsu.

A yanzu haka dai shugaban kasar na a birnin New Delhi, Inda  yake halatar taron kungiyar kasashe  ta G20  wanda  za’a gabatar daga ranar 9 zuwa  10  ga watan da muke ciki na Satumba.