On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Kano Da Wasu Jahohin Arewa 12 Zasu Fuskanci Ambaliyar Ruwa - Gwamnatin Najeriya

Gwamnatin tarayya ta fitar da sanarwar gargadin yiwuwar fuskantar ambaliya, inda ta ce jihar Kano da wasu jihohin Arewa 12 za su fuskanci ruwan sama kamar da bakin kwarya da ka iya haifar da ambaliya tsakanin 13 da 17 ga watan Satumba.

Sanarwar da Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya ta fitar ta lissafa garuruwa  50 a fadin Arewacin Najeriya  da ambaliyar ka iya shafa.

Wasu daga cikin jihohin da garuruwan sun hada da Sumaila da Kunchi a Kano sai Argungu a jihar Kebbi da Bindawa da Jibia da Kaita a jihar Katsina sai kuma Kontagora da Mashegu da sabuwar Bussa a jihar Neja da kuma wasu sassa a jihar Kwara da sauransu.

Hukumar ta ce saboda karuwar tumbatsar kogin Benue da Neja, an shawarci al’ummomin da ke kusa da Bayelsa da su dauki matakan kariya nan da kwanaki masu zuwa.