On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Kano Pillars Ta Lallasa Katsina United 2-1

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta lallasa kungiyar kwallon kafa ta Katsina United da ci 2-1 a gasar share fage ta shekarar 2023 a filin wasa na Sani Abacha dake kofar mata Kano.

‘Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Katsina United Andrew Idoko ne ya fara ciwa Katsina kwallo a cikin mintuna ashirin da shida na wasan.

An tafi hutun rabin lokaci ne da ci 1-0 a kungiyar kwallon kafa ta Katsina United na kan gaba.

Bayan dawowa dan wasa Rabi'u Ali aka Pele ya yi azama idan ya farkewa Sai masu gida.

Usman Gali wanda ya shiga wasan daga benci ya zura ta biyu a mintuna saba’in da takwas wadda ta ba su maki mafi girma.

Mai horas da ‘yan wasan Kano Pillars Abdu Maikaba ya ce gasar ta zama zakaran gwajin dafi domin kungiyarsa ta kara yin shiri kafin gasar firimiyar Najeriya ta 2023/2024 mai zuwa.

Maikaba ya bayyana jin dadinsa akan yadda ’yan wasansa suka taka rawar gani a wasanni biyu da suka buga kawo yanzu a gasar.

Kwamishinan matasa da wasanni na jihar Katsina Alhaji Yusuf Jirdede na daga cikin dubban masoya kwallon kafa da suka kalli wasan.