On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Kano Ta Samu Gagarumin Cigaba Da Sauye-Sauye Karkashin Gwamnatin Ganduje - Mai Martaba Sarki Aminu Ado

Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya yabawa gwamnan jihar Kano mai barin gado, Abdullahi Ganduje bisa goyon bayan da yake baiwa masarautar.

Sarkin ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai wa Gwamnan ziyarar Sallah a wani bangare na Hawan Nassarawa a gidan gwamnati.

Ya ce Kano ta samu gagarumin ci gaba da sauye-sauye a gwamnatin Ganduje, yana mai addu’ar Allah ya ci gaba da yiwa gwamna jagora da daukaka a cikin ayyukansa na gaba.

Ya kuma bukaci al’ummar jihar Kano da su bayar da hadin kai sosai domin samun nasarar kidayar jama’a da za a gudanar a kasar nan.

Da yake mayar da jawabi, Gwamna Ganduje wanda mataimakinsa Dakta Nasiru Yusuf Gawuna ya wakilta, ya ce gwamnatin ta yaba da irin gudunmawa da masarautar Kano ke  bayarwa kawo yanzu.