On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Kada Wani Abu Ya Samu Obi, El-Rufai - Atiku

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar

Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar African Democratic Congress (ADC), Atiku Abubakar, ya ce kare rayuka da haƙƙin 'yan adawa na daga cikin manyan alamomin dimokuradiyya, yana mai gargadin cewa kada a bari wani abu ya samu Peter Obi.

A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin sadarwa, Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku ya ce gwamnatin tarayya ya kamata ta tabbatar da tsaron dukkan shugabannin adawa maimakon mayar da martani da zagi ga masu sukar ta.

Ya kuma kara da cewa kama ta yayi gwamnatin dimokuradiyya ta maida hankali wajen amsa suka da hujjoji da kuma nuna dattako.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya kuma yi kira da a saki tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, yana mai cewa kowane dan Najeriya na da hakkin samun adalci, kariya a gaban doka kuma a ɗauke shi a matsayin marar laifi har sai kotu ta tabbatar da akasin haka.

Atiku ya bukaci gwamnatin tarayya ta daina mayar da hankali kan rikicin siyasa, ta fi karkata ga magance matsalolin tsaro, sace-sacen mutane, yunwa da talauci, yana mai cewa tarihi zai tuna da gwamnati ne bisa yadda ta kare rayukan jama'a da kuma tabbatar da adalci, maimakon fada da 'yan adawa ba kamar yadda yace tana yi a yanzu.

Comments

Add a comment

Log in to the club or enter your details below.

A Biyo Mu a Shafukan Sada Zumunta

Today's Weather

  • Kano

    Sunny intervals

    High: 34°C | Low: 22°C