On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Karancin Takardun Kudi Na Tunzura 'Yan Najeriya - NLC

Kungiyar kwadago ta kasa NLC, ta bukaci gwamnatin tarayya da babban bankin Najeriya, CBN, da su lalubo hanyoyin magance matsalar karancin naira da ‘yan Najeriya ke fuskanta  a halin yanzu.

Kungiyar ta NLC ta ce rashin mutunta gargadin daga CBN da Gwamnatin Tarayya  na nuna cewa da gangan suke tunzura ‘yan Najeriya.

Ya bayyana karancin a matsayin abin kunya, yana mai cewa uzuri ba zai kara karbuwa ba akan matsalar.

Shugaban NLC,  Joe Ajaero, wanda ya yi wannan gargadin a Abuja a wata ganawa da manema labarai ya ce an kure hakurin ‘yan Najeriya.

Ya kara da cewa babu wata gwamnati da ke jawo wa ‘yan kasarta irin wannan matsanani, kuma tana sa ran su yi shiru na tsawon lokaci.