On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Karbar Na Goro Yasa Farashin Dabbobi Suka Ta Shi

RAGO

Shugaban kungiyar masu sana’ar sayar da Dabbobi a birnin Calabar, Alhaji Isyaka Mohammed, Ya ce yana ware naira milyan daya cikin aljihunsa, domin bada cin hanci a shingayen binciken ababen hawa dake kan hanya, domin ganin an wuto masa da dabbobinsa da ya dauko daga yankin Arewacin kasar nan zuwa jihar Cross River dake kudancin kasar nan.

Mohammed  ya baiyana haka ne ga manema Labarai, lokacin da yake tsokaci  kan farashin  Raguna a  wannan  lokacin da  shagalin babbar  sallah.

Shugaba,  Ya yi zargin cewar  an samu tashin farashin raguna ne, bawai saboda janye  tallafin man fetir  ba,  sai dai kawai, saboda   kudin nagoro  da ake karba daga hannunsu akan hanya  daga  Arewa  zuwa kudancin kasar  nan.

Ya kuma kara da cewar  manyan motocin dake daukar masu dabbobi daga Arewa zuwa  kudu suna amfani ne da  man dizal,  wanda  farashin  ke cigaba da sauka  sannu a hankali,  a saboda  haka  babban kalubalen da suke  fuskanta, shi ne  yawan  karbar  nagoro daga  hannunsu akan hanya.