On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

'Karin Wasu 'Yan Najeriya 143 Da Suka Makale A Kasar Libiya Sun Dawo Gida Najeriya

YAN NAJERIYA

Karin wasu Yan Najeriya 143 da suka makale a kasar Libiya sun dawo gida a ranar Talata, inda suka sauka filin tashi da saukar jiragen sama na Murtala Muhammad dake birnin Ikko.

Shugaban Hukumar bada agajin gaggawa  ta kasa,  Mustapha Ahmed ya baiyana cewa, an sauke  mutanen da aka dawo dasu gidan ne ta filin tashi da saukar jiragen dakon kaya dake  cikin filin jirgin saman.

Ahmed yace mutanen sun hada da Manyan mutane 96 Sai Kananan Yara 8 Da wani jariri  1 sai kuma manyan Mata 36  da kuma wata karamar yarinya tare da wata Jaririya.