On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Karin 'yan majalisar dokokin jihar Kano guda 3 sun canza sheka daga jam'iyyar APC zuwa NNPP

'yan majalisar dokokin jihar Kano na cigaba da canza sheka daga jam'iyyar APC zuwa NNPP

Karin yan majalisun dokokin jihar Kano guda 3 sun canza sheka daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa jam’iyyar NNPP.

Wata sanarwa da daraktan yada labaran majalisar dokokin ta jihar Kano, Uba Abdullahi ya sanyawa hannu, tace bayanin hakan na kunshe a cikin wasiku mabanbanta da ‘yan majalisar suka aikewa kakakin majalisar a ranar Laraba, inda suka shaida masa hukunci su na canza shekar.

Kakakin majalisar ya karanta Wasikun nasu masu dauke da kwanan wata 5/5/2022, inda yay i musu fatan alkhairi a madadin sauran mambobin majalisar.

‘Yan majalisun da suka sauya shekar sun hadar da;

1. Hon. Abdullahi Iliyasu Yaryasa, mai wakiltar Tudun Wada

2. Hon. Muhd Bello Butu Butu, mamba mai wakiltar kananan hukumomin Tofa/Rimin Gado.

3.Hon.Kabiru Yusuf Ismail, mai wakiltar karamar hukumar Madobi.