On Air Now

ZANGON MARAICEN LAHADI

6:00pm - Midnight

Kasurgumin 'Dan Ta'adda Kachalla Ya Mutu a Hannun Sojojin Najeriya

Dakarun tsaron hadaka da ke taimakawa jami'an tsaro wajen yaki da 'yan ta'adda da masu garkuwa da mutane a Arewa maso Yamma sun kashe fitaccen shugaban 'yan bindiga, Kachalla Sani Yellow, wanda ake zargi da jagorantar hare-hare, satar shanu, garkuwa da mutane da kuma cin zarafin mata a jihar Zamfara.

Rahotanni sun ce an kashe Sani Yellow ne bayan wani shiri na kwanton bauna da aka gudanar bisa bayanan sirri, yayin da yake wata kasuwa domin karbar kudaden shanun da aka sace da kuma tattaunawa kan kudin fansar wasu mutane.

Bayan mutuwarsa, wasu fayafayen bidiyo da suka bazu sun nuna wasu daga cikin dakarun hadakar suna jan gawarsa akan babur, yayin da suke murnar nasarar da suka samu.

Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa Sani Yellow na daga cikin fitattun shugabannin 'yan bindiga da ke addabar yankunan Anka da Bukkuyum da Maru da wasu sassan jihar Zamfara.

Ana kuma zarginsa da jagorantar hare-hare kan kauyuka, sace daruruwan mutane domin neman kudin fansa, da kuma tilasta wa mabiyansa cin zarafin mata da aka yi garkuwa da su idan iyalansu sun kasa biyan kudin fansa.

A halin da ake ciki, rundunar 'yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da kashe Kachalla Sani Yellow, amma ta ce ba ita ce ta gudanar da aikin ba.

Kakakin rundunar, Yazid Abubakar, ya ce abin da rundunar za ta iya tabbatarwa shi ne mutuwar shugaban 'yan bindigar, yayin da jami'an tsaro suka kara sanya ido a yankunan da abin ya shafa domin dakile duk wani yunkurin daukar fansa daga mabiyansa.

Comments

Add a comment

Log in to the club or enter your details below.

A Biyo Mu a Shafukan Sada Zumunta

Today's Weather

  • Kano

    Sunny intervals

    High: 35°C | Low: 23°C