On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Ko Kun San Abunda Ya Haddasa Zaben Inconclusive A Jihar Kano ?

ZABEN INCONCLUSIVE A KANO

Kamishinan hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC na jihar Kano, farfesa Riskuwa Arabu Shehu, ya bayyana dalilan da suka sa aka ayyana zaben gwanan jihar Kano na shekarra 2019, a matsayin wanda bai kammala ba.

A wata ganawa da manema labarai a yau, ya bayyana rashin kammaluwar  zaben a bisa dalilin yawan kuri’un da aka soke, sunfi  yawan tazarar da manyan yan takarar biyu,  Abba Yusuf na PDP, da Abdullahi Ganduje na APC,  suka samu.

Da yake jawabi bayan shekaru 3 da yin zaben, Riskuwa yace  ba’a dauki matakin ba ne domin  ‘daga  kafa ga jamiyya mai mulki, kamar yadda wasu ke zargi a jihar kano, sai dai kawai tsari ne da doka ta tanada.

A ranar 11 ga watan Maris na 2019, baturen zaben gwamnan jihar  jihar farfesa Bello Shehu, ya bayyana sakamakon zaben gwamnan  na karshe, a matsayin wanda bai kammala ba.