On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Kotu ta Aike da Tsohon Shugaban Kotun Da'ar Ma'aikta Gidan Gyaran Hali

Babbar Kotun Birnin Tarayya da ke Maitama ta bayar da umarnin tsare tsohon Shugaban Kotun Da'ar ma'aikata ta Kasa, Danladi Umar, a gidan gyaran hali na Kuje bayan gurfanar da shi kan zargin cin hanci da rashawa.

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta gurfanar da Umar kan tuhume-tuhume guda hudu, inda ta zarge shi da amfani da mukaminsa wajen amfanar da kansa.

Hukumar ta ce ya karɓi naira miliyan 5.5 da kuma miliyan shida ta asusun bankin matarsa daga wasu 'yan kwangila da suka gudanar da ayyuka ga CCT.

EFCC ta kuma zarge shi da umurtar wani ɗan kwangila ya biya naira miliyan 2.43 kuɗin makarantar 'yarsa a Jami'ar Baze da ke Abuja. Sai dai Danladi Umar ya musanta dukkan tuhume-tuhumen da ake masa.

Mai shari'a Peter Kekemeke ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 15 ga Yuli domin sauraron buƙatar belin wanda ake tuhuma, bayan lauyoyin EFCC sun nemi lokaci domin mayar da martani kan takardar neman belinsa.

Comments

Add a comment

Log in to the club or enter your details below.

A Biyo Mu a Shafukan Sada Zumunta

Today's Weather

  • Kano

    Sunny intervals

    High: 34°C | Low: 22°C