On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Kotu Ta Ba Atiku Izinin Kaiwa Tinubu Sammace ta Hannun Jam'iyyar APC

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ba tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, izinin kai wa Shugaba Bola Tinubu takardun ƙarar da ya shigar ta hannun jam’iyyar APC.

Mai Shari’a Inyang Ekwo ne ya bayar da umarnin yayin da yake yanke hukunci kan buƙatar Atiku ta musamman, bayan lauyansa, O.T. Omotayo-Ojo, ya bayyana cewa an kasa kai wa Shugaban Ƙasar takardun ƙarar kai tsaye, don haka suka nemi kotu ta amince da wata hanyar daban ta isar da takardun.

Atiku da jam’iyyar ADC sun shigar da ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/1888/2026, inda suke neman kotu ta hana Tinubu da APC shiga zaɓen shugaban ƙasa na 2027, bisa zargin cewa an gabatar wa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, takardar shaidar kammala bautar kasa (NYSC) ta bogi.

Masu ƙarar sun kuma nemi kotu ta umarci INEC ta cire sunan Tinubu da APC daga jerin ’yan takara da jam’iyyun da za su shiga zaɓen shugaban ƙasa, yayin da kotu ta ba su wa’adin kwanaki bakwai domin kai wa Tinubu takardun ta hannun APC, sannan ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 28 ga Satumba domin cigaba da duba batun.

A gefe guda, Tinubu da APC sun musanta zargin gabatar da takardar NYSC ta bogi, suna kuma neman kotu ta yi watsi da ƙarar, yayin da INEC ma ta kalubalanci sahihancin shari’ar, tare da neman a yi watsi da ita bisa wasu dalilai na doka.

Comments

Add a comment

Log in to the club or enter your details below.

A Biyo Mu a Shafukan Sada Zumunta

Today's Weather

  • Kano

    Thunder storm

    High: 34°C | Low: 22°C