On Air Now

ZANGON MARAICEN LAHADI

6:00pm - Midnight

Kotu Ta Bada Umarnin Cigaba Da Tsare Murja Kunya A Gidan Gyaran Hali

MURJA IBRAHIM KUNYA

Kotu a nan Kano ta bada umarnin cigaba da tsare Murja Ibrahim Kunya a gidan Gyaran Hali.

Kotun ta  ce a cigaba da tsare ta har zuwa ranar  16   ga  watan fabarairun da muke  ciki, ina  za'a dawo domin cigaba da zaman kotun.

Ana zarginta  da yin kalaman rashin  da'a  wanda suka  sabawa  tarbiya  da kuma yanayin  zamantakewar  al'umma.

Zauren malaman jihar Kano ne  suka kai karar ta wata Kotun shari'ar musulunci dake garin Bichi a nan kano, Inda kuma  'yansanda  suka  dakume ta  kamar  yadda  Wakilinmu Bashir  Faruk  Durumin Iya    ya ruwaito  mana.